Gwamnatin Burkina Faso ta ce an kashe mutane 36 a wani harin ta’addanci a yankin arewa ta tsakiya na kasar.
An bayyana cewa wata kungiyar mayaka ce ta kashe mutane 32 a wata kasuwar kauyen Nagraogo a yammacin Litinin, sannan suka kara kashe mutum hudu a yayin wani ahri kusa da garin Alamou.
A ranar Talata, majalisar dokokin kasar ta kada kuri’a ka samar da masu aikin sa-kai domin yakar kungiyoyin ta’addanci.
Kafafen yada labarai na cikin gida sun ruwaito cewa za a bai wa masu aikin sa-kan horon farko irin na sojoji.