‘Yan bindiga sun sace tsohon jami’in hukumar tsaro na DSS, Peter Unogwu wanda aka fi sani Naraguta a jihar Binuwe kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Wanda aka sace din yana kula da Otel Igumale, hedikwatar karamar hukumar Ado dake jihar Binuwe. Peter Unogwu yana tafiya ne a titin Otukpo zuwa Utonkon-Igumale, inda wadanda ake zargin ‘yan bindiga ne suka tare motarsa suka zaro shi da karfi da yaji suka tafi da shi ya zuwa wani wuri wanda ya zuwa hada rahotan nan ba a tantance ba.
Wata majiya wanda ya bayyana kansa a matsayin Onazi Agbo ya shaidawa jaridar Punch cewa; tsohon jami’in DSS din an sace shi ne a yayin da yake tafiya a titi.
Majiyarmu ta labarto cewa; wanda aka yi garkuwa da shi din ya taba rike mukamin shugaban tsaro (CSO) na Kamfanin Chevron Nigeria Limited. Agbo ya kara da cewa; “Yana zuwa ne daga Otukpo ne zuwa Igumale, a yayin da doshi Igumale, sai kawai wadansu ‘yan bindiga suka tare shi suka fito da shi da karfi suka tafi da shi. Lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na yammacin ranar Laraba.” In ji shi.
Ya zuwa hada wannan rahoton, ‘yan bindigar ba su tuntubi iyalan wanda suka yi garkuwa da shi ba.
Da majiyarmu ta tuntubi Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Binuwe, DSP Catherine Anene, ya tabbatar da faruwar lamarin. Inda ya ce a halin yanzu jami’an ‘yan sanda sun baza komarsu domin cafko ‘yar garkuwar.
Anene ya kara da cewa; “Tsohon jami’in DSS din an sace shi a ranar Laraba. Jami’anmu tuni suka baza komarsu wajen kamo masu garkuwa da jama’a din.”