Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), ta bukaci gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta yi koyi da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan wajen warware yajin aikin da ake yi.
Malamai sun fara Yajin aikin a ranar 14 ga Fabrairu, 2022, kan gazawar gwamnati na cika bukatun kungiyar.
Yanzu haka dai yajin aikin ya shafe fiye da watanni shida ana gwabzawa da gwamnatin tarayya, ministocin ilimi da na kwadago, inda aka samu matsala wajen cimma matsaya.
Shugaban ASUU, Emmanuel Osodeke, a wata hira da AIT’s Focus Nigeria, ya yi ikirarin cewa gwamnatin Jonathan ta shiga wata tattaunawa ta sa’o’i 14 domin warware matsalar.
KARANTA ANAN; Jigawa@31: Gwamna Badaru Ya Yabi Sule Lamiɗo Da Karin Wasu Mutane
“Ya kamata gwamnati ta bi hanyar Goodluck Jonathan. Kuma a cikin dare ɗaya, mun yi wannan taron na awanni 14.
Jami’o’i na cikin wani yanayi na kalubale, don babu ajujuwan zama, babu damar gudanar da wasu aikace aikace na cikin gida, babu abubuwan zama, kuma mun duba dukkan batutuwa kuma mun warware shi cikin sa’o’i 14.
“Idan wannan gwamnati za ta iya fitar da wata tawaga mai karfi, idan shugaban kasa ba zai iya zuwa ba, to ya hada karfi da karfe ko mutanen da ba sa cikin wadanda ke fadin karya a halin yanzu.
“Mutanen da ke son kasar nan. Ba dole ba ne su kasance a cikin gwamnati. Idan za ku iya hada wannan abu mu hadu mu duba yadda za mu magance wannan matsala ta kasa,” in ji Osodeke.
A wani labarin kuma: Sojojin Da Suka Hallaka Shiek Goni Aisami Za’a Gurfanar Dasu A Kotun Fararen Hula
Rundunar sojin Najeriya ta ce za a mika sojojin biyun da ta kora, kuma ake zargin suna da hannu wajen kashe Sheikh Goni Aisami ga rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Yobe domin gurfanar da su a gaban kotu.
Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Asabar.