Babban daraktan hukumar kare hakkin jama’a ta Civil Society Legislative Advocacy Center (CISLAC), Auwal Ibrahim Musa (Rafsanjani), ya bukaci ‘yan Najeriya da su dorawa Hukumar Kwastam ta kasa NCS da Hukumar Shige da Fice ta Kasa (NIS) alhakin kwararar makamai a cikin al’umma da kuma ta’addanci a cikin kasar. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito
Musa wanda ya koka da yadda ake samun yawaitar ‘yan fashi da makami a kasar nan, ya bayyana cewa, aikin da kundin tsarin mulki ya ba hukumar kwastam da ta shige da fice ya kunshi duba kaya da mutanen da ke shigowa cikin kasar nan a tashoshin ruwa da na kasa daban-daban.
Rafsanjani, wanda ya bayyana hakan a yayin wani taron karawa juna sani na kwana daya kan kafafen yada labarai da rahotonnnin su ‘Defence Anti-corruption Reportage, Civic Space and Oversight’ a turance, da aka gudanar a Legas, ya kuma bukaci a gudanar da bincike kan makaman da wasu suke rikewa a matsayin na kariya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ka Kwaikwayi Tsarin Goodluck Don Kawo Karshen Yajin Aikin Da Muke Yi – Kiran ASUU Ga Buhari
Ya bayyana cewa, da a ce sassan biyu na gwamnati sun sadaukar da rabin makamashin da ake amfani da su wajen gudanar da ayyukan fasakwaurin shinkafa da daskararrun kaji wajen duba shigowar makamai da kuma baki, da yaki da ‘yan fashi da makami.