Alhaji Tukur Mamu, jagoran masu sasantawa tsakanin ‘yan bindiga da fasinjojin da aka yi garkuwa da su daga wani jirgin kasa mai zuwa Kaduna a watan Maris, an kama shi a birnin Alkahira, babban birnin kasar Masar, tare da iyalansa.
Mamu wanda ke kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudiyya don gudanar da aikin Hajji, an tsare shi na tsawon sa’o’i 24 a filin jirgin sama na Alkahira, kuma ana shirin dawo da shi gida Nijeriya.
Da yake zantawa da jaridar Daily trust, Mamu ya ce ya bar Najeriya ne a ranar Talata, kuma bayan da jami’an tsaron Masar suka bincike shi, ba a gano wani abu na laifi a hannunsa ba.
Karanta kuma: Jirgin Abuja-Kaduna: Sauran Da Suka Rage Suna Cikin Wani Hali —- Mai Shiga Tsakani
Mamu ya zayyana wani shiri da gwamnatin Najeriya ta yi na tsare shi a wata kasa kamar yadda aka yi wa dan gwagwarmayar ‘yancin Yarbawa, Sunday Igboho, amma hakan bai samu ba saboda gwamnatin Masar din ta gano cewa takardunsa na gaske ne.
Daily Trust ta ruwaito Mamu ya fice daga tattaunawa da ‘yan bindigar bayan ya yi zargin cewa gwamnatin Najeriya na yi masa barazana da kuma yunkurin bata masa suna.
Har yanzu gwamnati ba ta mayar da martani kan ikirarin Mamu ba amma wasu na zarginsa da hada baki da ‘yan ta’adda, zargin wanda ya musanta.
A wani labarin kuma: Rashin Aikin Yi: Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Matasa, Mata Kan Neman Dabaru
Gwamnatin Tarayya ta bukaci matasa da mata da su kara samun sana’o’i don samawa kansu ayyukan yi da inganta hanyoyin samar da kudaden shiga a kasar nan.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Sakatariyar dindindin ta ma’aikatar kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire Monilola Udoh ce ta yi wannan kiran a yayin wani shirin horar da ma’aikata kan albarkatun halittu da aka shirya wa matasa da mata marasa aikin yi a garin Ibadan na jihar Oyo, in ji sanarwar da ma’aikatar ta fitar.