Hukumar kula da aikin ‘yan sanda ta kudiri aniyar ci gaba da daukar sabbin jami’an ‘yan sanda duk kuwa da matakin da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta dauka.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa an samu rashin jituwa tsakanin hukumar ta PSC da hukumar NPF, musamman babban sufeton ‘yan sanda, Usman Baba kan daukar sabbin ‘yan sanda aiki.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ku Yiwa Allah Kukawo Karshen Yajin Aiki— Shugaban C&S Ya Roki FG Da ASUU
A ranar 15 ga Agusta, 2022, PSC ta buɗe wata hanyar shiga yanar gizon ta don ɗaukar ‘sabbin jami’an yan sanda aiki.
A martaninta, NPF ta ce tallan ba ta dace da tsarin daukar ‘yan sanda ba, don haka ya kamata a yi watsi da su.
A cikin rashin jituwar, ma’aikatan PSC sun shelanta yajin aikin sai baba ta gani, inda suka bukaci shugaban hukumar Mista Musiliu Smith ya yi murabus.
A ranar Laraba, kakakin hukumar Mista Ikechukwu Ani, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce hukumar ta PSC za ta ci gaba da daukar sabbin jami’ai aikin, inda ya kara da cewa hukumar ba ta da niyyar yin watsi da aikin da kundin tsarin mulkin kasar ya ba ta na daukar ‘yan Najeriya aikin ‘yan sanda.
Ya ce, “Hukumar ita ce kawai hukumar da shari’a ya dora mata alhakin daukar ma’aikata a duk wuraren uku na rundunar ‘yan sandan Najeriya – kwastabul, Cadet Inspector, da Cadet Assistant Sufiritanda.
“Hukumar na son bayyana cewa shafin daukar ma’aikata da aka bude a ranar Litinin, 15 ga watan Agusta, 2022, tana ci gaba da aiki, inda mutum sama da 60,000 suka yi ragista kawo yanzu. Za a rufe tashar ne a ranar 26 ga Satumba, 2022. Ya kamata ’yan Najeriya masu sha’awar ci gaba da amfani da wannan damar domin yin aiki a rundunar ‘yan sandan Najeriya su yi ragista kafin ranar, domin hukumar ba ta da niyyar yin kari kan wa’adin.”
Ani ya kuma bayyana cewa, bangaren gudanarwa da shugaban hukumar suna aiki tare don kare kundin tsarin PSC.
A WANI LABARIN KUMA: Gwamnan Legas Ya Maye Gurbin Kwanishinan Da Yayi Murabus
Gwamnan jihar Legas, Mista Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da tsohon kwamishinan ayyuka na musamman da hulda da gwamnatocin tarayya, Tayo Bamgbose-Martins, a matsayin sabon kwamishinan tsare-tsare da raya birane na jihar.
Kwamishinan yada labarai da dabaru na jihar Mista Gbenga Omotoso ne ya sanar da hakan a ranar Laraba a Alausa, Ikeja.