Gwamnan jihar Legas, Mista Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da tsohon kwamishinan ayyuka na musamman da hulda da gwamnatocin tarayya, Tayo Bamgbose-Martins, a matsayin sabon kwamishinan tsare-tsare da raya birane na jihar.
Kwamishinan yada labarai da dabaru na jihar Mista Gbenga Omotoso ne ya sanar da hakan a ranar Laraba a Alausa, Ikeja.
Ya ce, “Ina shaida muku cewa Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya sake tura Tayo Bamgbose-Martins a matsayin sabon kwamishinan tsare-tsare da raya birane.
KARANTA WANNAN LABARIN: Uba Sani Ya Jagoranci Tantace Mutanen Da Buhari Ya Turo Domin Basu muƙami a CBN
“Shi ne zai maye gurbin Idris Salako, wanda ya yi murabus. Don haka, Bamgbose-Martins yana zuwa cikin wani sabon yanayi na ƙwarewa da ke fitowa daga Ma’aikatar Ayyuka na Musamman.
“Bamgbose-Martins ƙwararren injiniya ne wanda ya shafe shekaru 33 yana samun gogewa a matsayin ma’aikacin gwamnati.”
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa tsohon kwamishinan, Salako, ya yi murabus a ranar Litinin, bayan rugujewar wani bene mai hawa bakwai a yankin Victoria Island dake jihar ta Legas.
A WANI LABARIN KUMA: Ku daina yaudarar Ƴan Najeriya, ba Cigaban da Tinubu ya kawo a Legas – Jigon APC
Tunde Bank-Anthony, jigo a jam’iyyar APC mai mulki a Legas, ya gargadi magoya bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023, Bola Ahmed Tinubu, da su daina yaudarar ƴan Najeriya game da nasarorin da Tinubu ya samu a jihar. .
A yayin da yake magana a gidan Talabijin na Channels Television’s Sunrise Daily a ranar Laraba, Bank-Anthony ya ce magoya bayan Tinubu na yi wa ‘yan Najeriya karya a wani yunkuri na samun karbuwa ga dan takararsu.