Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya rattaba hannu kan dokar sanya alama da tallace-tallace na shekarar 2022 da wasu kudirorin dokoki uku. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito
Dokar ta tilasta wa ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyun siyasa a zabe mai zuwa su biya kowannen su Naira miliyan 10 kafin a ba su izinin manta Hoton su na siyaya wato fosta, allunan talla da tutoci a Kogi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hajj 2022; Gwamnan Zamfara Ya Bada Umarnin Maidowa Alhazan Jihar Naira 50,000
Yan takarar Gwamna da Sanata da Majalisar Wakilai da na Majalisar Tarayya za su biya Naira milkiyan, 5, Mikkiyan 2, Milkiyan 1 da kuma naira 500,000.
Bello ya ce sabbin dokokin da aka sanya wa hannu za su saukaka tsaftar muhalli da karuwar kudaden shiga ga jiihar.
Ya bukaci ‘yan majalisar dokokin jihar da su zakulo duk wasu dokokin da aka amince da su a baya da aka sanya wa hannu amma ba a aiwatar da su daga ma’aikatu daban-daban ko hukumomi ko kuma jami’an tsaro domin a hada gwiwa da sa ido da tantancewa.
Gwamnan ya kuma bukaci majalisar da ta ci gaba da yin aiki tare da sauran bangarorin gwamnati domin yi wa al’umma hidima.
Sauran dokoki guda uku da aka rattabawa hannu sune Dokar da za ta samar da tsare tsaren tabbatar da dokar tallace-tallace ta2022; dokar da ta tanadi sokewa da sake fasalin otal da hukumar yawon shakatawa na 1995; da dokar kafa hukumar kula da yawon bude ido ta jihar Kogi da sauran batutuwan da suka shafi hakan.
A nasa jawabin, kakakin majalisar dokokin jihar Kogi, Matthew Kolawole, ya bada tabbacin goyon bayan majalisar domin samun ci gaban kudaden shiga da ake samu a jihar.
A WANI LABARIN KUMA: Za Mu Ci Tarar Duk Kamfanin Jirgin Saman Da Ke Saida Tikitin Da Dala— FG
A ranar Laraba ne gwamnatin tarayya ta umurci hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya NCAA da ta sanyawa kamfanonin jiragen sama na kasa da kasa takunkumin da aka ce sun ki sayar da tikiti a Naira domin kare muradun ‘yan Najeriya.
Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ne ya sanar da hakan ga manema labarai bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya.