Yanzu-Yanzu: Ƴan Bindiga sun Hallaka Ƴan Sanda 3 a Enugu
Wani hari da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kai a daren Laraba, ya yi sanadin mutuwar ‘yan sanda akalla uku a jihar Enugu.
DAILY POST ta samu labarin lamarin ya faru ne a titin Chime Avenue, New Haven, karamar hukumar Enugu ta Arewa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tinubu, Atiku, Obi, Da Sauransu Zasu Biya Naira Milliyan 10 Kafin Lika Fastocinsu A Jihar Kogi
Wata majiya ta bayyana cewa ‘yan bindigar da suke cikin motar sienna, sun bi motar hilux din ‘yan sandan inda suka bude musu wuta.
An ce uku daga cikin jami’an sun mutu a nan take.
A wani labarin kuma: Yanzu-Yanzu: Jami’an DSS Sun Afka Gidan Mamu Dake Kaduna
Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun kai farmaki gidan wani mai tattaunawa da yan ta’addan da aka kama, Tukur Mamu a Kaduna da sanyin safiyar yau Alhamis. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
‘Yan sandan sun zo ne a cikin motoci kusan 20 a wani abin da wani shaida ya bayyana.