Majalisar dokokin jihar Kano, ta buƙaci ƴan majalisar tarayya da ke wakiltar Kano da su yi gaggawar yin kira ga gwamnatin tarayya don ta ɗauki dangane da ɓallewa da Dam ɗin Tiga ya yi.
Hakan dai ya biyo bayan ƙudurin haɗin gwiwa da dan majalisar Ƙiru kuma mataimakin shugaban majalisar Kabiru Hassan Dashi da na Bebeji Abubakar Uba Galadima da wakilin Rano Nuruddeen Alhassan Ahmad suka gabatar.
Da yake gabatar da ƙudurin, Alhaji Kabiru Hassan Dashi, ya ce, akwai buƙatar ɗaukar matakin gaggawa kan madatsar ruwan ta Tiga tun kafin ta haifar da mummunar ɓarna.
KARANTA ANAN: FRSC Ta Dakatar Da Jami’anta Daga Rakiyar Ayarin Yan Siyasa
Da yake ƙarin haske kan ƙudurin, ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Rano Alhaji Nuruddeen Danlami Alhassan, ya ce zuwa yanzu a yankin nasa na Rano an samu mutuwar mutane biyar tare da rushewar gidaje fiye da sittin.
Shi kuwa a tasa gudunmawar, shugaban masu rinjaye na majalisar Alhaji Labaran Abdul Madari, buƙatar majalisar ya yi da ta tuntuɓi gwamnatin tarayya kan iftila’in kasancewar hukumar ta Hadejia Jama’are a ƙarƙashin ta take.
A wani labarin kuma, ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Doguwa Salisu Ibrahim Muhammad, ya gabatar da ƙudurin gaggawa na buƙatar gwamnatin jihar Kano ta kai musu ɗauki dangane da karyewar gada sakamakon ambaliyar ruwa a hanyar shiga dajin Falgore.
A cewar ɗan majalisar duk da cewa titin na gwamnatin tarayya ne, amma akwai buƙatar gwamnatin jiha ta kai ɗaukin gaggawa kafin hanyar ta gagara bi.
Bayan gabatar da ƙudurin nasa da kuma tsokaci daga mambobin majalisar ne kuma ta buƙaci gwamnatin jihar Kano da ta yi gaggawar kai wa gadar ɗauki har ma da yankunan da suka gamu da iftila’i sakamakon ambaliya a damina bana.
Haka kuma yayin zaman na yau, majalisar ta karɓi rahoton kwamitinta na harkokin muhalli kan dokar magance gurɓatar yanayi.
A wani labarin kuma: Yan sanda Sun Bindige Wani Da Ake Zargun Mai Garkuwa Da Mutane Ne
Jami’an hukumar ‘yan sanda reshen jihar Edo sun kashe wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne a yayin wani artabu da ‘yan sanda a jihar Edo.
Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a dajin Ughiole da ke karamar hukumar Etsako ta Yamma a jihar a ranar Lahadi.