Sabon shugaban kasar Kenya, Mr Willaim Samoei Ruto ya dauki rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasar Kenya na Biyar.
Babban magatakardan ma’aikatar shari’a ne ya rantsar da sabon shugaban, yayin da taron daka gudanar yau, wanda ya samu halartar dubban mutane daga cikin da wajen kasar.
Yayin da Abokin adawar Mista Ruto, wato Raila Odinga bai halarci bikin ba, inda ya ce yana da “damuwa mai yawa” game da sakamakon zaben.
KARANTA ANAN: An Gano Wasu Gwamnonin PDP 4 Da Yiwa Tinubu Aiki
Baya ga rantsar da Mista Ruto, an kuma rantsar da mataimakinsa Rigathi Gachagua.
An gudanar da bikin ne a filin wasan birnin Nairobi mai daukar nauyin mutum 60,000.
Shugabannin kasashen da ke makwabtaka da Kenya na cikin wadanda suka halarci bikin rantsar da sabon shugaban.
A wani labarin kuma: Osinbajon Ya Ketare Zuwa Kenya Domin Wakiltar Buhari
Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bar Abuja zuwa Nairobi, domin wakiltar shugaban kasa Muhammadu Buhari a wajen bikin rantsar da shugaban kasar Kenya.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa hakan na kunshe cikin wata sanarwa da aka sanya wa hannu, ta hannun babban mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban kasa kan harkokin yada labarai da yada labarai, Laolu Akande.