Kotun koli ta yi watsi da hukuncin da aka yanke kan wanene halastaccen dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Ebonyi a babbab zaben 2023 da ke tafe.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Kotun mai alkalai biyar karkashin jagorancin mai shari’a Amina Augie, ta sanar a ranar Larabar nan cewa za a yanke hukuncin da karfe 3 na yammacin yau bayan sauraren gabatar da karar da lauyoyi suka gabatar ga bangarorin da ke cikin karar mai lamba: SC/CV/ 939/2022 da Ifeanyi Chukwuma Odii ya shigar.
Karanta kuma: Ba A Kore Ni daga Takarar Sanatan Ebonyi Ta Kudu Ba — Umahi
Kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) ya ruwaito cewa Mista Odii da Sanata Joseph Obinna Ogba sun kafale ne a wata takaddamar shari’a kan wanda aka zaba a matsayin dan takarar jam’iyyar a zaben shekara mai zuwa a zaben fidda gwani na jam’iyyar da ya gudana a lokuta daban-daban a jihar.
Jaridar SOLACEBASE ta rawaito cewa, A baya-bayan nan ne kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta bayyana Sanata mai wakiltar Ebonyi ta tsakiya, Ogba a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar a jihar.
Amma Mista Odii, bai gamsu da hukuncin kotun ba, ya shigar da kara a kotun koli.
Kotun mai alkalai biyar ta tsaya tsayin daka domin yanke hukunci bayan lauyoyin bangarorin sun amince da tsarinsu tare da gabatar da hujjojinsu.(NAN)
A wani labarin kuma: Ambaliyar Ruwa Ta Afkawa Gidaje 200 A Garin Makurdi – SEMA
Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje sama da 200 a garin Makurdi, kamar yadda wani jami’in gwamnati a jihar Benue ya bayyana.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Sakataren zartarwa na Hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Benue (SEMA), Dakta Emmanuel Shior, ne ya bayyana hakan a garin Makurdi ranar Larabar nan a wajen rabon kayan agaji na wata-wata ga ‘yan gudun hijirar.