Cibiyar dakile cututtuka masu yaduwa ta Nijeriya, NCDC sun tabbatar da samun mutum na farko da yake dauke da cutar Koronabairos a jihar Sakkwato.
Cikin sabbin jihohin daga Arewa da aka samu cutar a karon farko cutar korona ta
da Sokoto da Gombe.
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Sokoto ya gabatar da jawabi a wani taron manema labarai inda ya ce za a mayar da mutumin da cutar ta shafa zuwa cibiyar kebe marasa lafiya ta Amanawa.
Hukumar dakile cututtuka masu yaduwa a Najeriya ta ce adadin masu fama da cutar ya zuwa daren Litinin ya kai 665, bayan samun karin mutum 38 masu dauke da cutar a fadin kasar.
Sai dai wani labari mai karfafa gwiwa shi ne mutum 18 ne rigis suka warke daga cutar a ranar Litinin din cewar alkaluman NCDC, inda yanzu haka mutum 198 daga cikin 665 suka warke.
Wannan karo jihar Kano ce ta fi samun mutanen da cutar ta sake kamawa da 23, inda adadin masu annobar ya kai 59 a cikin kwana 10.