• About Us
  • Blog
  • Gwamnatin Jihar Kano ta ce ana gabda fara ginin masana’antun Iskar Gas a Jihar
  • Home
Saturday, June 3, 2023
  • Login
Dimokuradiyya
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio
No Result
View All Result
Dimokuradiyya
No Result
View All Result
Home Labarai

‘An Wulakanta Ni Da Ake Jingina Ni Da Mukamin Abba Kyari’

Mustapha Haruna Dabai by Mustapha Haruna Dabai
April 21, 2020
in Labarai, Siyasa
Reading Time: 3 mins read
1 0
0
2
SHARES
16
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Daya daga cikin mutanen da ake rade-radin cewa suna cikin makusantan shugaban Najeriya da za su iya maye gurbin Malam Abba Kyari, ya ce lokaci ya wuce ga mutum irinsa ya karbi wani aikin gwamnati.

Alhaji Ismaila Isah Funtua ya ce: “Abin da na ji a raina…Na dauki wannan jita-jita (a matsayin) wulakanci. An wulakanta ni”.

Ya ce lokacin da aka kori gwamnatin farar hula a 1983 (Jamhuriya ta biyu) yana minista. “Har wani yau ya yi tunanin a kawo sunana cikin (wadanda za a iya nadawa) shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa?”

Tun bayan rasuwar Malam Abba Kyari ranar Juma’a ne, wasu mutane suka fara zayyana sunayen makusantan Shugaba Buhari, suna cewa a cikinsu ne za a nada magajin Abba Kyari.

Shi dai Isma’ila Isah Funtua na cikin manyan mutane guda uku da ake ganin na-hannun dama ne ga shugaban Najeriya, hasali ma su ne wasu ke wa lakabi da ‘cabal’ wato da su ake kulla komai na gwamnati mai ci.

Ko da yake, tsohon ministan ya sha musanta wannan ikirari.

Isma’ila Funtua ya ce: “Na yi aikin En’E, na yi aikin gwamnati, na shiga siyasa har na tashi na kai matsayin minista a kasar nan”.

Mutumin da ya yi minista 1983 zuwa yau kusan shekara nawa ke nan? An tasam ma shekara 40. Kuma sai a ce wai ka je a nada ka mukami. Wanne aiki za a ba ni, yanzu? In ji shi.

Ya ce ai ya fi karfin a ba shi wani aiki. “Ni mai daukar mutane aiki ne, tun da na kafa wuraren da jama’a za su samu abinci da iyalansu”.

A cewarsa shedanci ne ya sa wasu kawai suke kama sunan wani jigo su ce a ba shi aiki don kuwa ba sa la’akari da abubuwan da ya yi a baya, da kuma ko zai iya aikin, ko ma ya fi karfin aikin da ake ambata.

“Irin abin nan ne da ake cewa mutum ya wuce lokacin da za a ba shi aiki. Aiki yanzu ai sai ‘ya’yanmu ko kannenmu,” in ji Alhaji Isma’ila Funtua.

Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya masu irin wannan tunani su rika mutunta kawunansu da kasarsu.

A cewarsa idan mutum irinsa kullum zai makale a gwamnati sai ta ba shi aiki, to me suke so ‘ya’yansu da kannensu su yi?

An tambaye shi, to idan Shugaba Buhari ya bukaci ya karbi mukamin don ya taimaka wa gwamnatinsa. Sai ya ce shi ma ba zai fara ba, “don ya san ba zan karba ba”.

Isma’ila Funtua ya ce Najeriya ba ta yi lalacewar haka ba, a cewarsa masu rade-radin suna mayar da sha’anin mulkin kasa kamar wasa.

“Idan ka duba ma sunayen da suke rubatawa…. Haba jama’a!”

Ya ce idan yau kana da aikin kwamiti, ka duba mutum irinsa da wadansu “daidai da ni da wadanda suka fi ni, ka ce don Allah ku duba abu kaza ku ba ni shawara. Sai a yi, a ba ka shawara.”

“Amma dai ba dai mu yi aiki a ce a ba mu albashi ba,” in ji Isma’ila Funtua.

Daga Shafin BBC HAUSA

Previous Post

Mutum 665 Ke Da Korona A Nijeriya

Next Post

A Karon Farko #Coronavirus Ta Bulla A Sokoto

Next Post

A Karon Farko #Coronavirus Ta Bulla A Sokoto

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result
  • Ya ce mun shi Dillalin Motoci ne, bayan mun yi aure na gane Makanike ne

    Ya ce mun shi Dillalin Motoci ne, bayan mun yi aure na gane Makanike ne

    2600 shares
    Share 1040 Tweet 650
  • Batun Dakatar Da Opay Da Palmpay, CBN Ya Bayyana Gaskiyar Zance

    2342 shares
    Share 937 Tweet 586
  • Da Ɗumi-Ɗuminsa: Ƙazamin Rikici Ya Kaure Tsakanin Shugaban Ƙungiyar CAN Da Isa Ashiru Kudan

    2129 shares
    Share 852 Tweet 532
  • Sai na yi lalata da kai na kwanaki 4 babu ƙaƙƙautawa sannan zan taimaka maka, Wata mata ga saurayi

    1904 shares
    Share 762 Tweet 476
  • Ga Irinta Nan: Budurwa Ta Koka Bayan Saurayinta Ya Ƙi Amsar Cikin Da Ya Ɗirka Mata

    1438 shares
    Share 575 Tweet 360
Tallafi: Tinubu Ne Kadai Zai Iya Sanya Dokar Kayyade Farashin Man Fetur – Falana ga NNPCL

Tallafi: Tinubu Ne Kadai Zai Iya Sanya Dokar Kayyade Farashin Man Fetur – Falana ga NNPCL

June 2, 2023
Da Dumi-Dumi: EFCC Ta Kame Wata Tsohuwar Minista Kan Badakalar Zunzurutun Kudi Biliyan N2bn

Da Dumi-Dumi: EFCC Ta Kame Wata Tsohuwar Minista Kan Badakalar Zunzurutun Kudi Biliyan N2bn

June 2, 2023
Rikicin PDP: Kotu Ta Tabbatar Da Korar Ayu Daga Matsayin Shugaban Jam’iyyar Na Kasa

Rikicin PDP: Kotu Ta Tabbatar Da Korar Ayu Daga Matsayin Shugaban Jam’iyyar Na Kasa

June 2, 2023
Ta Zama Matuƙiyar Jirgin Sama Bawan Kwashe Shekara 10 Tana Burin Hakan

Ta Zama Matuƙiyar Jirgin Sama Bawan Kwashe Shekara 10 Tana Burin Hakan

June 2, 2023
Murna Har Kunne: Dan Takarar Gwamnan NNPP da Wasu Mambobi 2000 Sun Koma APC

Murna Har Kunne: Dan Takarar Gwamnan NNPP da Wasu Mambobi 2000 Sun Koma APC

June 2, 2023
Da Dumi-Dumi: An Sanya Ranar Gudanar da Zaben Kananan Hukumomi a Jihar Yobe

Da Dumi-Dumi: An Sanya Ranar Gudanar da Zaben Kananan Hukumomi a Jihar Yobe

June 2, 2023
Tallafi: Tinubu Ne Kadai Zai Iya Sanya Dokar Kayyade Farashin Man Fetur – Falana ga NNPCL
Labarai

Tallafi: Tinubu Ne Kadai Zai Iya Sanya Dokar Kayyade Farashin Man Fetur – Falana ga NNPCL

June 2, 2023
Da Dumi-Dumi: EFCC Ta Kame Wata Tsohuwar Minista Kan Badakalar Zunzurutun Kudi Biliyan N2bn
Labarai

Da Dumi-Dumi: EFCC Ta Kame Wata Tsohuwar Minista Kan Badakalar Zunzurutun Kudi Biliyan N2bn

June 2, 2023
Rikicin PDP: Kotu Ta Tabbatar Da Korar Ayu Daga Matsayin Shugaban Jam’iyyar Na Kasa
Labarai

Rikicin PDP: Kotu Ta Tabbatar Da Korar Ayu Daga Matsayin Shugaban Jam’iyyar Na Kasa

June 2, 2023
Tallafi: Tinubu Ne Kadai Zai Iya Sanya Dokar Kayyade Farashin Man Fetur – Falana ga NNPCL

Tallafi: Tinubu Ne Kadai Zai Iya Sanya Dokar Kayyade Farashin Man Fetur – Falana ga NNPCL

June 2, 2023
Da Dumi-Dumi: EFCC Ta Kame Wata Tsohuwar Minista Kan Badakalar Zunzurutun Kudi Biliyan N2bn

Da Dumi-Dumi: EFCC Ta Kame Wata Tsohuwar Minista Kan Badakalar Zunzurutun Kudi Biliyan N2bn

June 2, 2023
Rikicin PDP: Kotu Ta Tabbatar Da Korar Ayu Daga Matsayin Shugaban Jam’iyyar Na Kasa

Rikicin PDP: Kotu Ta Tabbatar Da Korar Ayu Daga Matsayin Shugaban Jam’iyyar Na Kasa

June 2, 2023

Twitter

Archives

Recent Posts

  • Tallafi: Tinubu Ne Kadai Zai Iya Sanya Dokar Kayyade Farashin Man Fetur – Falana ga NNPCL
  • Da Dumi-Dumi: EFCC Ta Kame Wata Tsohuwar Minista Kan Badakalar Zunzurutun Kudi Biliyan N2bn
  • Rikicin PDP: Kotu Ta Tabbatar Da Korar Ayu Daga Matsayin Shugaban Jam’iyyar Na Kasa

Quick Links

  • Tsaro
  • Siyasa
  • Labarai
  • Wasanni
  • Kasuwanci
  • Rikicin Duniya

Contact Us

info@dimokuradiyya.com.ng

0809 912 4425 +234 809 912 4425

No. 218 Mogadishu layout Kaduna City Center Ahmadu Bello way kaduna. Kaduna, Nigeria 800273

Copyright © 2023 Dimokuradiyya Media Services LTD.

No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio

Copyright © 2023 Dimokuradiyya Media Services LTD.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In