Kungiyar daliban Najeriya ta kasa ta ce mambobinta za su tare hanyar filin jirgin saman kasa da kasa na Nnamdi Azikwe, dake Abuja da kuma filin jirgin sama na Kaduna a yau Laraba.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa zasu dauki wannan mataki ne a wani bangare na zanga-zangar nuna adawa da matakin da kungiyar malaman jami’o’i ke yi.
A ranar Litinin din da ta gabata daliban sun tare hanyoyin shiga filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Ikeja, inda fasinjojin jirgin da sauran su suka gamu da tsaiko.
KARANTA ANAN: Magoya Bayan Bola Tinubu, Sun Yabawa Sanata Uba Sani Kan Tafiya Da Mata A Harkar Mulki
Da yake magana da a ranar Talata, shugaban kungiyar NANS wajen zangar zangar janye yajin aikin ASUU Olumide Ojo, ya ce daliban ba su yi zanga-zanga a tashar jirgin ruwa ta Apapa kamar yadda aka shirya yi a ranar Talata ba don ba su damar tsara dabarun da kuma shirya zanga-zangar mai tasiri a ranar Laraba ba.
Shima da yake jawabi, shugaban NANS na kasa Usman Barambu, yace daliban Najeriya sun gaji da zaman gida, yana mai cewa yakamata gwamnati ta bude jami’o’in domin dalibai su koma makaranta.
A halin da ake ciki, a ranar Talata ne gwamnatin jihar Kaduna ta gargadi daliban kan yunkurin tare hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Shi kuwa Babban Manajan Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Tarayyar Najeriya, Faithful Hope-Ivbaze, ya ce an tura jami’an tsaro zuwa filin jirgin Abuja.
A wani labarin kuma: Yan Boko Haram 17 Sun Mika Wuya Tare Da Iyalansu
Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa ‘yan ta’addar Boko Haram goma sha bakwai da suka hada da iyalansu sun mika wuya ga sojojin Bataliya ta 151.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa jami’an sune wadanda aka tura zuwa lBanki-Junction a karamar hukumar Bama a jihar Borno.