Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa ‘yan ta’addar Boko Haram goma sha bakwai da suka hada da iyalansu sun mika wuya ga sojojin Bataliya ta 151.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa jami’an sune wadanda aka tura zuwa lBanki-Junction a karamar hukumar Bama a jihar Borno.
Rundunar ta bayyana hakan ne a ranar Talata ta shafinta na Twitter tana mai cewa, yawan mika wuya da ‘yan ta’addan da iyalansu suke yi, ya biyo bayan wani sabon farmakin da dakarun soji na Operation Hadin Kai suka kai a yankin Arewa maso Gabas.
KARANTA ANAN: Kafa ‘Yan Sandan Jihohi Babu Makawa — Inji Kakakin Majalisar Dattawa
A cewar rahotanni, wani babban mai zartar da hukuncin kisa na bangaren Shekau, Bashir Bulabuduwaye, ya mika wuya ga sojojin Najeriya kwanan nan.
Bulabuduwaye, tare da matansa da ‘ya’yansa, an ce sun mika wuya ga dakarun Operation Hadin Kai da ke Baking a karamar hukumar Bama a jihar Borno.
DIMOKURAƊIYYA ta kuma samu labarin cewa kawo yanzu kimanin mayakan Boko Haram 79,000 da kuma wadanda ba mayakan Boko Haram ba ne suka mika wuya ga dakarun Operation Hadin Kai a wurare daban-daban.
A wani labarin kuma: Majalissar Akwa Ibom Ta Ayyana Kujerun ‘Yan Majalisar Biyu A Matsayin Wadanda Babu Kowa
Majalisar dokokin jihar Akwa Ibom a ranar Talata yayin zamanta ta bayyana kujerun mazabar Esit Eket da Ikono a matsayin wadanda babu kowa bayan da suka fice daga jam’iyyar, PDP zuwa jam’iyyar, YPP.
Kujerun sun kasance karkashin Rt.Hon.Usoro Akpanusoh, mai wakiltar mazabar Esit Eket da Hon. Asuquo Nana Udo, mai wakiltar mazabar Ikono.