Rundunar yan sandan jihar Kano ta ce za ta gurfanar da Dan Chinan nan Mr Gheng Quanrog gaban Kotu bisa zarginsa da kashe Ummukulsum da aka fi Sani da Ummita.
Idan za a iya tunawa Mista Quanrong ya bi Ummukhulsum ne har gidan iyayenta ya caccaka mata wuka, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwarta, a ranar Juma’ar da ta gabata.
A yau Laraba ne dai za a gurfanar da wanda ake tuhumar a gaban kotu, yayin da jami’an ‘yan sanda suke ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
KARANTA ANAN: Sanatoci Sun Yi Gum Da Batun Tsige Shugaba Buhari Bayan Dawowar Su Daga Hutu
Labarin kisan matashiyar ya tayar da hankulan jama’a a jihar, dama kasa baki daya, yayin da har yanzu wasu ke ta mamakin yadda lamari ya kasance.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Wadda aka hallaka ɗin abaya sun taɓa yin soyayya da Quanrong kafin ta yi aure wanda daga baya suka rabu da mijinta.
Tuni dai gwamnatin Kano ta sha alwashin tabbatar da an yiwa Marigayiyar adalci.
A wani labarin kuma: Yajin Aikin ASUU: NANS Zata Tare Hanyar Filayen Jiragen Saman Abuja/Kaduna
Kungiyar daliban Najeriya ta kasa ta ce mambobinta za su tare hanyar filin jirgin saman kasa da kasa na Nnamdi Azikwe, dake Abuja da kuma filin jirgin sama na Kaduna a yau Laraba.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa zasu dauki wannan mataki ne a wani bangare na zanga-zangar nuna adawa da matakin da kungiyar malaman jami’o’i ke yi.