Gwamnatin tarayya ta haramta tafiye-tafiye a tsakanin jihohi a wani mataki na dakile yaduwar cutar COVID-19 a fadin kasarnan.
Dr Osagie Ehanire, ministan ma’aikatar lafiya ta Nijeriya shi ne ya tabbatar da hakan a ranar Laraba a Abuja, a yayin da yake yiwa kwamitin shugaban kasa kan lura da dakile yaduwar cutar Korona a Nijeriya.
Ehanire ya ce dukkanin mutanen da aka same su da cutar Korona za a lura da su ne a jihohin da aka gwada su aka same su da cutar domin ganin an magance yaduwar cutar zuwa wadansu wurare.
Ya shawarci PPMVs da su kauracewa cewa za su magance masu cutar Korona, idan ba haka ba za a kwace lasisin ayyukansu.