Jam’iyyar APC reshen jihar Jigawa ta dakatar da dan majalisar dokokin jihar mai wakiltar mazabar Kanya Babba, Honarabul Usman Haladu Isah, bisa laifin yiwa jam’iyyar zagon kasa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar manema labarai da shugaban jam’iyyar na karamar hukumar Babura Isa Ubale da shugaban jam’iyyar na mazabar Kanya Babba suka sanyawa hannu tare da aikewa manema labarai.
Sanarwar ta ce ana zargin dan majalisar da yiwa jam’iyyar zagon kasa gabanin zaben 2023 da kuma rashin mutunta dattawan jam’iyyar.
KARANTA ANAN: An Gargaɗi Tinubu Da APC Kan Amfani Da Kuɗi Wajen Raba Kan Kiristoci
Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewa dan majalisar jihar ya rasa tikitin tsayawa takara a hannun Ibrahim Hashim Kanya a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC na zaben 2023 mai zuwa.
Ubale ya ce, dukkan jiga-jigan jam’iyyar na mazabar sun amince da dakatarwar. Dakatarwar ta fara aiki ne daga ranar 24 ga watan Satumban 2022, har sai an kammala bincike don ci gaba da daukar mataki.
Sanarwar ta kara da cewa an aike da kwafin takardar dakatarwar ga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar.
A wani labarin kuma: Yan Najeriya Sama Da Miliyan 100 Na Cikin Ƙangin Talauci, Ina Da Maganin Hakan – Inji Peter Obi
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party Peter Obi ya koka kan yadda ake ci gaba da fuskantar matsin rayuwa a wannan lokaci, da yan Najeriya ke gwammace kida da karatu ta fuskar rayuwa.
Peter Obi a wajen wani taron kan harkar Kasuwanci da aka shirya a Jihar Legas, ya nake kolin halin da yan Najeriya ke ciki, da kuma irin rawar da zai taka wajen kawo musu mafita.