Rundunar ‘yan sanda a Legas ta fara gudanar da bincike kan mutuwar wani karamin yaro da ya mutu bayan da aka yi masa allura a wani asibiti da ke unguwar Ogombo a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO) a Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Kasa NAN lamarin a ranar Alhamis din nan.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Hundeyin ya ce ‘yan sanda sun samu labarin lamarin, amma babu wanda ya bayar da rahoto a hukumance game da lamarin
KARANTA KUMA: Rundunar Yan Sanda Ta Ankarar Da Jami’anta Kan Barazanar Kai Hari A Legas
“Eh, muna sane da lamarin. Mahaifin marigayin ya zo ofishin yan sanda amma ya ki rubuta wani bayani.”
“Su ma ma’aikatan asibitin sun zo ofishin ba tare da yin wani bayani ba. Don amfanin kowa, an tura su zuwa CID na jihar don gudanar da bincike mai kyau,” inji shi.
NAN ta ruwaito cewa wani mutum yana kuka a faifan bidiyo da ya yadu inda ya koka kan yadda wata ma’aikaciyar jinya ta yi wa dansa allurai hudu, wanda ba a ambaci sunanta ba kuma ya mutu sakamakon maganin da aka yi masa.
Jaridar Solacebace ta rawaito cewa, Mutumin ya yi ikirarin cewa an yi wa dan wasu magunguna ne a ranar Laraba kuma ya yi amai bayan kowace allura.
Ya jaddada cewa wata ma’aikaciyar jinya ce ta yi wa yaron alluran hudu ba tare da yaron ya ci abinci ba kuma yaron ya mutu.
NAN ta kara da cewa faifan bidiyon ya kuma nuna gawar yaron a kan gado tare da mahaifin na kuka a gefensa. (NAN)
A wani labarin kuma: Karramawa Ta Kasa: Buhari Ya Amince Da Matsayin CON Ga Gwamna Zulum
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da baiwa gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum kyautar lambar girmamawa ta CON (Commander of the Order of Niger).
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnati, Sanata George Akume ne ya bayyana hakan a wata wasika da ya aikewa gwamnan.