Fitacciyar jarumar nan ta Najeriya, Mercy Johnson ta bayyana dalilin da ya sa ta daina fitowa a fina-finan soyayya.
Fim ɗin Mercy Johnson na farko mai suna ‘The Maid’ wanda ya kawo ta cikin masu shirya fina-finai da dama yayin da ta fito a fina-finai da dama da suka haɗa da fina-finan barkwanci da na soyayya.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Matashiyar ‘yar shekara 38 mai ‘ya’ya hudu ta bayyana dalilinta na kin daukar irin wadannan ayyuka fina-finan ne aurenta da Yarima Odianosen Okojie.
A cewarta, mijin nata bai ji dadin ganin yadda ta yi irin wannan yanayin ba, don haka sai da suka yi aure ta daina.
Jaridar Diamondcelebrities ta rawaito cewa, Jarumar ta hadu da mijinta a karon farko a shekarar 2008 a jirginta na zuwa kasar Faransa, kuma sun yi aure a ranar 27 ga watan Agusta, 2011.
A wani labarin kuma: An kama masu haƙar Ma’adinai 12 ba bisa ka’ida ba a Ogun
Jami’an hukumar tsaro ta So-Safe Corps mallakin jihar Ogun sun kama wasu masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba 12 a yankin Ogun ta Gabas.
DAILY POST ta samu labarin cewa an kama mutanen 12 a tsakanin ranakun 28 zuwa 30 ga watan Satumba, “a lokacin da suke satar dukiyar gwamnatin jihar.”