Shafin Worldometers ya labarto cewa kasar Amurka ce ke da mafi yawa na wadanda suka mutu sakamakon cutar korona a duniya.
Jumillar adadin yanzu ya zarta 65,000 da kuma fiye da mutum miliyan 1.1 da aka tabbatar sun harbu da cutar ya zuwa hada rahoton nan.