Rahotanni daga Taraba sun ce daya daga cikin majinyatan cutar korona ta tsere daga cibiyar da aka killace su.
Kafar talabijin ta Channels ta ce kwamishinan lafiya Innocent Vakkai kuma jagoran yaki da cutar korona a jihar ne ya sanar da haka ne a yayin ganawa da manema labarai.
Ya ce wata mata ce ta tsere, kuma suna kan kokarin gano ta.
Zuwa yanzu mutum takwas aka tabbatar da sun kamu da cutar korona a jihar Taraba