Gwamnatin jahar Oyo, ta samu matsaya kan mafi karancin albahshi na Naira 30,000, biyo bayan zaman da akayi da kungiyoyin kwadago a babbar sakatariyar jahar.
An yi Zaman ne da wakilan gwamnati da na NLC,TUC, da kuma JNC, hakan ya Biyo Bayan saka hannun da shugaba Muhammadu Buhari, ya yi a ranar 18 ga watan Afrilu kan mafi karancin albahshi na Naira Dubu talatin.
Tun a ranar 24 ga watan Afrilu gabanin ranar ma’aikata ta bana aka fara wannan zama tare da Manyan mambobin kungiyoyi daban-daban na Ma’aikata a jihar.
Inda suka roki Gwamnatin jahar kan tabbatar da tsarin sabon Albashin, tare Kuma da gargadi ga Gwamnatin kan cewa ya kamata ne Karin ya fara aiki nan take.
Sakataren Gwamnatin Jihar Olalikan Alli, Wanda ya jagoranci bangaren Gwamnati ya jaddada cewa jahar za ta bi duk tsarin da aka gindaya Mata ba tare da wata Tangarda ba.
Alli, ya cigaba da cewa muna jiran shugaban ma’aikatan jahar da ya fayyace mana komai Bisa tsari gabanin kaddamar da Wannan tsari kai tsaye.