Gwamnatin jihar Borno ta ce an sallami mutum 12 daga asibitin koyarwa ta Jami’ar Maiduguri bayan sun warke daga cutar annobar korona.
Maitaimakin gwamnan jihar Umar Kadafur wanda ke jagorantar yaƙi da cutar korona ne ya sanar da haka a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi.
Sanarwar ta ce tun a jiya aka sallami mutum biyu. Kuma yanzu majinyatan korona 22 ne ke jiran sakamakon gwaji ya fito domin sanin ko sun warke daga cutar kamar yadda rahoton Bbc Hausa ta labarto.