Gwamnatin jihar Kano ta kara mako guda kan dokar killace jihar Kano, a wani mataki na dakile yaduwar cutar Korona a jihar.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammed Garba shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a madadin gwamnatin a daren ranar Litinin.
Kwamishinan ya ce wannan daukar matakin ya zama dole bayan tattaunawar da suka yi da gwamnatin tarayya da wadansu masu ruwa da tsaki a kan harkar lafiya.
Gwamnatin ta ce an dauki wannan matakin ne domin ganin an dakile yaduwar cutar Korona a tsakanin hulda ta mutum da mutum, wanda ya ce tana daya daga cikin abin da ke sanya cutar yaduwa. Inda ya nemi al’umma da su kara hakuri bisa wannan mataki da aka sake dauka.
Sannan ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da sanya takunkumin fuska, tare da bai wa juna tazara da kuma ci gaba da wanke hannuwa.
NCDC sun tabbatar jihar Kano na da mutum 666 da suke da cutar Korona, inda mutum 32 suka mutu, yayin da mutum 571 ne suke ci gaba da samun kulawa sakamakon suna da cutar har yanzu.