Hedikwatar rundunar sojin Nijeriya ta ce sun hallaka ‘yan ta’addan Boko Haram a dajin Sambisa dake jihar Borno. Inda suka ce sun yi wannan nasarar ne bayan harin sama da rundunar sojin sama ta Operation Lafiya Dole (OPLD) suka kai a ranar Juma’a.
Jami’in hulda da kafafen watsa labarai na Hedikwatar Sojin, Manjo Janar Enenche shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja a ranar Asabar. 00
Enenche ya ce sun samu wannan nasarar ne bayan bayanan sirrin da suka tattara.