Rfi Hausa sun labarto cewa; Dakta Osagie Ehanire ya ce sakamakon binciken da suka gudanar a baya baya nan ya nuna cewar, adadin mata masu ciki dake zuwa awo ya ragu da sama da kashi 50 cikin 100, kwatankwacin raguwa daga adadin mata miliyan 1 da dubu 300, zuwa mata masu juna biyu dubu 655, yayin da kuma adadin matan dake zuwa asibiti domin haihuwa ya ragu daga miliyan 4 zuwa miliyan 2 a fadin Najeriya.
Binciken da hukumar Nijeriya mai tattara bayanan alkalumman da suka shafi fannin lafiya ta gudanar, ya kuma gano cewar, adadin kananan yaran da ake kaiwa asibiti domin samun allurorin rigakafi shi ma da ya ragu da kusan kashi 50, yayin da yawan mutanen dake zuwa asibiti don duba lafiyarsu bisa ra’ayinsu ya ragu daga akalla dubu 158 da 374, zuwa kasa da dubu 99.