2023: Atiku zai gana da Gwamnonin G-5 – Okowa
Gwamnan jihar Delta kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Ifeanyi Okowa, ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar, zai gana da gwamnonin G-5, domin kawo karshen matsalolin da suka dabaibaye jam’iyyar.
Sanata Okowa ya kuma karyata ikirarin cewa jam’iyyar ta yanke shawarar yin watsi da Gwamnonin Integrity G-5 da Gwamna Nyesome Wike ke jagoranta tare da yin gaba da zaben shugaban kasa a 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ya sharbi kuka: Yadda matashi ya kai wa budurwarsa ziyara bazata, ya sha mamakin abin da ya gani
Okowa, wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba a Yenagoa bayan taron kungiyar gwamnonin Kudu-maso-Kudu tare da Gwamna Udom Emmanuel na Akwa Ibom, Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo da kuma mai masaukin baki, Sanata Douye Diri, ya ce PDP za ta warware matsalar dukkan batutuwan nan ba da jimawa ba, kuma ba za su bari Gwamnonin G-5 su fice daga jam’iyyar ba.
A cewar Gwamna Okowa, “Ba shakka maganar cewa Jam’iyyar za ta yi watsi da Gwamnonin G-5 ba gaskiya ba ne. Suna cikin danginmu kuma na yi imani akwai batutuwa kuma ana halartar waɗannan batutuwa. Nan ba da jimawa ba dan takarar shugaban kasa zai gana da gwamnoni. Suna cikin iyali kuma ba za mu bar su su tafi ba. Babu shakka, akwai abubuwa da yawa da ake sanyawa don sulhunta dukkan bangarorin da kuma tafiya tare a matsayin daya”.
Sai dai kuma gwamnan jihar Ribas, Nyesome Wike, shugaban gwamnonin G-5, bai fito fili yayi wata magana ba.
Tun da farko, Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya shaidawa manema labarai cewa gwamnonin sun kai ziyarar ne domin jajanta wa takwaransu na jihar Bayelsa, Gwamna Douye Diri kan bala’in ambaliyar ruwa da ya afku a jihar.
Obaseki ya kuma ce taron nasu ne domin gano yadda yakin neman zaben shugaban kasa ke gudana daga Okowa tare da maido da goyon bayansu ga ‘yan takarar shugaban kasa da mataimakinsa na jam’iyyar.
A wani labarin kuma: NAWOJ Ta Bukaci Mata Yan Jarida Su Karkata Kan Rahotannin Matsalolin Jinsi
Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya bayyana cewa jam’iyyar ta shirya tsaf domin lashe zaben gwamnan jihar da za a yi a shekara mai zuwa ta hanyar tsiya ko da tsiya-tsiya
Da yake jawabi a wajen kaddamar da yakin neman zaben fidda gwanin takarar gwamna na jam’iyyar da aka gudanar a Gaya, Abbas ya bayyana cewa APC, kasancewar jam’iyyar da ke jagorantar jihar, ba za a iya kayar da ita ba.