Yanzu-Yanzu: Masarautar Katsina Ta Dakatar Da Wani Hakimi
Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman, Ya Sanar Da Dakatar Da Makaman Katsina Hakimin Gundumar Bakori Ta Jihar Katsina, Alhaji Sule Idris Nadabo Daga Sarautar Har Sai An Gama Bincike.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Gwamna Uzodimma Ya Kori Shugaban Jami’ar Jihar Imo
Bayanin Hakan Na Kunshe A Cikin Wata Takardar Manema Labarai Da Aka Rabawa Manema Labarai A Katsina, Wadda Sakataren Majalisar Masarautar Katsina, Alhaji Bello Mamman Ifo Ya Sanya Hannu Yau Laraba.
A wani labarin kuma: Mun kwato Dala Biliyan 1 da aka sace – Malami
Babban Lauyan Najeriya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya bayyana cewa kawo yanzu gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta kwato kimanin dala biliyan 1 da aka sace daga shekarar 2015 zuwa 2022.
Malami ya bayyana hakan ne a fadar shugaban kasa dake Abuja yayin da yake zantawa da wakilin gidan gwamnatin jihar bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya na mako a ranar Laraba.