Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya kori mataimakin shugaban jami’ar aikin gona da kimiyar muhalli ta jihar Imo dake Umuagwo, Farfesa Patrick Egbule.
Bayanan sauke shugaban jami’ar ta fitone ta cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Cosmas Iwu ya raba wa manema labarai a Owerri, babban birnin jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Dumi: Tinubu Ya Isa Jihar Ebonyi, Don Kaddar Da Wani Aiki
An maye gurbin Egbule da Farfesa Christopher Chiedozie Eze, a matsayin mukaddashin mataimakin shugaban jami’ar nan take.
Sanarwar ta kara da cewa, “Gwamnan Jihar Imo, Mai Girma Sanata Hope Uzodimma, ya amince da tsige Farfesa Patrick Egbule a matsayin Mataimakin Shugaban Jami’ar Aikin Gona da Muhalli ta Jihar Imo, Umuagwo nan take.
“Saboda haka, bisa ga dokar da ta kafa jami’ar, Gwamnan ya amince da nadin Farfesa Christopher Chiedozie Eze a matsayin mataimakin shugaban riko na jami’ar noma da kimiyar muhalli ta jihar Imo, Umuagwo.”
“Yayin da Gwamna ya ke yiwa tsohon mukaddashin shugaban jami’ar fatan alheri a cikin ayyukansa na gaba, ya kuma tuhumi mukaddashin shugaban jami’ar Farfesa Chiedozie Eze da ya mika kansa ga mafi girman matsayi a harkokin tafiyar da makarantar.”
A wani labarin kuma, Zaben 2023: Bola Tinubu ya yi nasara a Kotu
Wata Babbar Kotun Tarayyar da ke Abuja ta yi fatali da bukatar soke takarar Bola Tinubu a zaben 2023.
Jam’iyyar Action Peoples Party (APP) ta maka jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai rike da tutar shugaban kasa kotu.
Shari’ar mai lamba FHC/UM/CS/124/2022 an Shigar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta kasa (INEC) a matsayin wanda ake kara na farko.