Mun kwato Dala Biliyan 1 da aka sace – Malami
Babban Lauyan Najeriya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya bayyana cewa kawo yanzu gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta kwato kimanin dala biliyan 1 da aka sace daga shekarar 2015 zuwa 2022.
Malami ya bayyana hakan ne a fadar shugaban kasa dake Abuja yayin da yake zantawa da wakilin gidan gwamnatin jihar bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya na mako a ranar Laraba.
KARANTA WANNAN LABARIN: ‘Yan sanda sun dira wani gida bayan jin ihun neman taimako, ashe tsuntsu Aku ne
Ministan shari’a ya ce an tura kadarorin da aka kwato zuwa sassa daban-daban na tattalin arzikin kasar da suka hada da rage radadin talauci.
“Tsakanin 2015 zuwa 2022, gwamnatinmu ta kwato kusan dala biliyan 1 da aka sace daga sassa daban-daban.”
Malami ya kuma bayyana damuwar gwamnati kan al’amuran da suka shafi kasafin kudi, wanda ya bayyana a matsayin abin damuwa, inda ya ce za a binciko duk wani matakin da ya dace don magance shi.
A wani labarin kuma: Da Dumi-Dumi: Tinubu Ya Isa Jihar Ebonyi, Don Kaddar Da Wani Aiki
Wata Babbar Kotun Tarayyar da ke Abuja ta yi fatali da bukatar soke takarar Bola Tinubu a zaben 2023.
Jam’iyyar Action Peoples Party (APP) ta maka jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai rike da tutar shugaban kasa kotu.
Shari’ar mai lamba FHC/UM/CS/124/2022 an Shigar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta kasa (INEC) a matsayin wanda ake kara na farko.