Ministan yada labaru, al’adu da yawon bude ido a Nijeriya, Alhaji Lai Mohammed, a jiya Asabar ne yake rokon ‘yan jarida da kafafen sadarwa da su taimaki gwamnatin tarayya wajen kokarinta kan yadi da ta’addanci a fadin Nijeriya. Ministan wanda ya samu wakilcin Darakta a ma’aikatan yada labaru, Mista Sunday Baba ya yi kiran ne a wajen bikin ‘2019 Biennial Conbention of the Nigerian Guild of Editors da ka gudanar a garin Ikeja, da ke jihar Legos.’ yana mai shaida cewar kafafen da ‘yan jarida suna da rawar da ya dace su taka wajen taimaka wa yaki da miyagu da baragurbi da suke cikin kasar nan. Lai Mohammed sannan ya kuma bukaci ‘yan jarida da su taimaki sojoji da gwamnati mai ci wajen kyautata zaman lafiya da zamantakewar al’umma domin tabbatar da kwanciyar hankali a tsakanin ‘yan kasa. A cewar shi; “A matsayinku na kwararru kan harkar watsa labaru hakki ne a wuyarku wajen kula da aiyukan gwamnati da tsare-tsarenta domin tabbatar da kyautata manufofi da gina kasa. “A don haka, gwamnati tana tsammanin ‘yan jarida a kowani lokaci za su ke bayar da shawarorin yadda za a inganta zaman lafiya, kwanciyar hankalin kasa, domin al’ummarmu su amfana da gwamnati da kuma yalwar zaman lafiya,” Inji shi. A sakonsa na fatan alkairi, gwamnan jihar Legas Mista Akinwunmi Ambode ya shaida cewar suka da hanyoyin da kafafen sadarwa suke bi suna taimakawa wajen kyautata tsarin gina jihar. Gwamnan da ya samu wakilcin kwamishinan yada labaru da tsare-tsare, Mista Kehinde Bamigbetan ya kara da cewa rokon ‘yan jarida da suke kara baiwa gwamnan jihar hadin kai domin ya samu cimma muradinsa na kyautata jihar Legas. “Daga cikin ababen da muka nazarta a shekaru hadun da suka gabata musamman wajen kaddamar da aiyukan sake fasali da aka samu tagomashi a zahirin gaskiya sun samu ne da sukar da kuka yi ta yi mana wanda yanzu jama’a suna gamsuwa aiwatar da aiyuka daidai da muradinsu,” A cewar shi. Shugaban tsangayar koyar da aikin jarida na jami’ar Legas, Farfesa Abigail Ogwezzy-Ndisika ta bayyana cewar da bukatar kafofin watsa labaru masu nagarta su yi kokarin magance matsalolin da suke addabar aikin jarida a wannan zamanin. Ogwezzy-Ndisika ta yi bayanin cewar sabbin kafafen sadarwar sun mamace al’ummarmu musamman ta yanar gizo-gizo wanda ta ce da bukatar kwararru a fannin su kara tusa kansu domin kada a gurbata musu aiki ta wadannan sabbin kafafen. Ta jero kadan daga cikin matsalolin da ‘yan jarida da gidajen jaridu suke fuskanta a daidai wannan lokacin da suka hada da karancin kudade (talauci) rashin ladabi ga wasu ‘yan jarida, da kuma shigar da ababe marasa kyau cikin harkar. Ogwezzy-Ndisika ta lura da cewar kasashen da suka ci gaba, sun ci gaba ne a sakamakon kyautata aiki da kuma tafiya daidai da zamaninsu. Ta ce, daga cikin sabbin kafafen da suka shigo a wannan zamanin da suke barazana wa ci gaban aikin jarida sun hada da Facebook, Twitter, Youtube, Google, Nairaline da sauran sabbin kafafen sadarwar zamani.