Fasto Yohanna Buru, shugaban kungiyar dawo da zaman lafiya a Nijeriya, ya shawarci ‘yan Nijeriya da su bai wa hukumomin tsaro cikakkiyar goyon bayan a kokarinsu na tabbatar da zaman lafiya a fadin kasarnan.
Fasto Buru ya nemi hakan ne a ranar Alhamis a yayin da yake bai wa jami’an tsaron sa kai na CJTF a Kaduna. Fasto Buru ya jaddada cewa bai wa jami’an tsaro goyon baya ne musamman ta hanyar ba su ingantattun bayanan da suka dace dangane da bata gari da wadanda ake zargi da miyagun laifuka, zai taimaka wajen kawo zaman lafiya da daidaiton al’amura a fadin kasarnan.
Faston ya ce yana da kyau a rika tallafawa hukumomin tsaro da kayan aiki musamman jami’an sa kai na al’umma kamar su C-JTF din domin ba su damar gudanar da ayyukansu cikin nasara.
Ya kuma shawarci Musulmi da Kirista dake jihar Kaduna da ma kasar baki daya da su rungumi dabi’ar tattaunawa wajen tabbatar da zaman lafiya a kasa baki daya.
Shugaban jami’an C-JTF, Shehu Dan-Tudu , ya jinjinawa Fasto Buru bisa wannan tallafi da suka samu daga gare shi, inda ya ce suna da jami’an a karkashin C-JTF din sama da dubu uku a fadin jihar.