Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya amince da karin kwanaki 8 a kalandar makarantu a zangon karatu na shekarar 2022/2023 a jihar.
Kwamishinan Ilimi na jihar, Mista Lawan Wakilbe, wanda ya tabbatar da hakan a ranar Juma’a a Maiduguri, ya ce amincewa da hakan ne don baiwa ma’aikata da daliban da suka cancanta damar gudanar da hakkokinsu na al’umma.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Dumi: Kamfanin NNPC Zai Fara Aikin Hako Man Fetur A Jihar Nassarawa
Ya ce gwamnati ta bayar da hutun kwanaki takwas don gudanar da babban zabe mai zuwa a watan Fabrairu, don kuma ba da damar amfani da makarantu a matsayin Cibiyoyin Kula da zaben.
NAN ya ruwaito cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta tsayar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya a ranar 25 ga watan Fabrairu, yayin da za a gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha a ranar 11 ga watan Maris.
A wani labarin kuma, Kotun Koli Ta Kori Basaraken Gargajiya Na Obong, Ta Ba Da Umarnin Asake Zabar Sabon Sarki
Kotun kolin Najeriya ta kori Obong na Calabar, Mai Martaba Sarkin Ekpo Okon Abasi-Otu V, a ranar Juma’a, 13 ga watan Janairu, kan karar da ta shafe tsawon shekaru 15, tare da bayar da umarnin a zabi wani sabon Sarki.
Shari’ar dai ta kasance tsakanin Obong na Calabar na yanzu, Mai Martaba Eze Ekpo Okon Abasi-Otu na Biyu wanda ke kan karagar mulki tun shekarar 2008, da kuma mai kalubalantarsa, Etubom Anthony Ani.