Rundunar ‘yan sandan jihar Benuwe a ranar Laraba ta gurfanar da wasu mutane Charles Fegha mai shekaru 40 da Tersoo Ayen mai shekaru 32 da kuma Bemdoo Igbahemba mai shekaru 29 a gaban wata kotun majistare mai lamba 3B dake Makurdi bisa zarginsu da hada baki, barna da kuma sata.
Dan sanda mai shigar da kara, Insifekta Kwegh Abugh, ya shaida wa kotun cewa wani Tarnongo Tiza, ma’aikacin Standard Organisation of Nigeria ne ya kai rahoton karar a ofishin leken asiri dake hedikwatar ‘yan sandan jihar Makurdi a ranar 29 ga watan Disambar shekarar 2022.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tsohon Shugaban APC da Daruruwan Magoya Bayan Jam’iyyar Sun Sauya Sheka Zuwa PDP
Abugh ya ce a ranar ne mai ba da labarin ya ajiye wasu bakinsa a otal din Trust Resort da ke lamba 3 Lucy Aluor street New GRA Makurdi sannan ya ajiye motarsa a gaban wurin saukar baki kafin ya shiga cikin otel din.
Ya ce risafshin din tana kusa da kofar otal inda ake iya ganin na’urar daudauka ta CCTV.
“Lokacin da yake wajen wurin risafshi, ya gano cewa gilashin kofar bayan motarsa an fasa su kuma an sace kudi zunzurutun kudi Naira dubu 900,000 daga motar,” in ji mai gabatar da kara.
Ya ce yayin binciken ‘yan sanda, Charles Fegha, Tersoo Ayen, da Bemdoo Igbahemba, an kama dukkan ma’aikatan Otal din Trust Resort da laifin aikata laifin.
Ya ce wadanda ake tuhumar sun saba wa sashe na 97, 329 da 288 na dokar Penal code na jihar Benue shekarar 2004.
Abugh ya ce har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin inda ya bukaci a ba shi karin lokaci domin kammala shi.
Sai dai a lokacin da aka gabatar da karar, wadanda ake tuhumar sun musanta dukkan zarge-zargen da ake yi musu.
Alkalin kotun, Misis Kadoom Gbasha, ta bayar da belin wanda ake zargin a kan kudi Naira 100,000 kowanne, tare da tsayayyen mutum daya a daidai wannan adadin, wanda dole ne ya kasance ma’aikacin gwamnatin jihar Binuwai.
Gbasha ta dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Fabrairu domin ci gaba da sauraren shari’ar.NAN
A wani labarin kuma, An Sako Dan Tsohon Shugaban Kasar Iran Bayan Shafe Shekaru Bakwai A Gidan Yari
Dan tsohon shugaban kasar Iran Akbar Hashemi Rafsanjani ya samu ‘yanci bayan ya shafe sama da shekaru 7 a gidan yari daga cikin shekaru 10 bisa samunsa da laifin zamba kamar yadda kafafen yada labaran Iran suka rawaito.
Mehdi Hashemi, mai shekaru 53, ya bar gidan yarin Evin na Tehran da yammacin jiya Talata, in ji lauyansa Vahid Abolmaali, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ISNA ya ruwaito.