Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce hukumar zabe ta kammala wani shiri na kada kuri’a ga Yan Najeriya dake zaune a kasashen waje. Kamar yadda Chennels TV ta ruwaito.
Yakubu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da lacca a zauren Chatham da ke birnin Landan a ranar Talata da yamma, kan batun ‘Zaben Najeriya na 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tsohon Shugaban APC da Daruruwan Magoya Bayan Jam’iyyar Sun Sauya Sheka Zuwa PDP
Da yake jawabi ga al’amuran da ke faruwa dangane da halasta jefa kuri’ar ga ‘yan Najeriya dake zaune a kasashen waje, Shugaban INEC ya bayyana fatan cewa za a kawar da matsalolin da doka ta hana ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje yin zabe daga karshe.
A cewar Yakubu, hukumar tana aiki ne kawai bisa tsarin dokokin zabe, wanda har yanzu shi ne babban dalilin da ya sa ba za ta iya aiwatar karbar kuri’ar zaben ’Yan najeriya dake zaune a kasashen waje ba a halin yanzu, kamar yadda shugabancinta ke so.
Idan za a iya tunawa, A shekarar 2017, Gwamnatin Tarayya, ta ce adadin ‘yan Najeriya da ke zaune a kasashen waje ya kai miliyan 17.
A wani labari kuma, An Gurfanar Da Wasu Ma’aikatan Otal Bisa Laifin Sace Kudaden Kwastomomi
Rundunar ‘yan sandan jihar Benuwe a ranar Laraba ta gurfanar da wasu mutane Charles Fegha mai shekaru 40 da Tersoo Ayen mai shekaru 32 da kuma Bemdoo Igbahemba mai shekaru 29 a gaban wata kotun majistare mai lamba 3B dake Makurdi bisa zarginsu da hada baki, barna da kuma sata.
Dan sanda mai shigar da kara, Insifekta Kwegh Abugh, ya shaida wa kotun cewa wani Tarnongo Tiza, ma’aikacin Standard Organisation of Nigeria ne ya kai rahoton karar a ofishin leken asiri dake hedikwatar ‘yan sandan jihar Makurdi a ranar 29 ga watan Disambar shekarar 2022.