Kwamitin tallafin kudi na majalisar dinkin duniya, UNFPA a ranar Litinin a garin Damaturu, ta tallafawa gwamnatin jihar Yobe da kayayyakin yaki da annobar cutar Korona.
Dr Homsuk Swomen, Jami’in shirin UNFPA shi ne ya mika kayayyakin da suka hada da takunkumin fuska guda 1,750 da kuma dogon abin hannu guda 2000 da gajere guda 800 sai abin wanke hannu guda 193.
Da yake magana a yayin mika kayayyakin, Swomen ya ce UNFPA har wala yau ta horas da jami’an gwamnatin jihar a bangare daban-daban domin bunkasa kwarewarsu. Inda ya ce UNFPA din ta dade tana gudanar da ayyukanta a arewa maso gabashin kasarnan tun kafin bayyanar ta’addanci a yankin, tare da tallafawa gwamnatoci daban-daban da suke yankin.