Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Juma’a 12 ga watan Yuni a matsayin ranar hutu domin tunawa da ranar Dimokuradiyya ta shekarar 2020.
Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, shi ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya a sanarwar da ya fitar.
Sanarwar wacce Sakataren ma’aikatar harkokin cikin gida ya sanyawa hannu, Georgina Ehuriah ya labarto minista Aregbesola na taya al’ummar Nijeriya murnar ranar dimokuradiyya ta kasarnan.
Ministan har wala yau ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su ci gaba da girmama gwagwarmayar da aka yi aka dawo turbar dimokuradiyya.
Ya jaddada cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da kokarinta wajen ganin ta yi yaki da annobar cutar Korona, inda ya nemi da ‘yan Nijeriya su bada hadin kai. Ya kuma nemi bukatar da yake akwai na ‘yan Nijeriya da su ci gaba da bin ka’idojin kariya daga kamuwa da Korona.