Kamfanin waya na 9Mobile ya ayyana Alan Sinfield a matsayin sabon shugaban gudanawar na kamfanin.
Kamfanin ya bayyana Alan a matsayin wani jajirtaccen shugaba, mai hangen nesa da sanin ya kamata, kuma wanda yake da kyakkyawan tarihin gudanar da aiki tare da kawo ci gaba ga kamfanin.
Har wala yau sun ce shugaba ne da yake da kwarewa tare da bankado hanyoyin jawo wa hankali kwastomomi zuwa ga kamfanin. Sannan sun bayyana shi a matsayin wani jagoran kawo sauyin ci gaba ga kamfanin.
9Mobile sun bayyyana hakan ne a wani rahoto da suka wallafa a shafinsu. Inda suka kara da cewa ya rike shugabanci a kamfanin tun daga 2006, wanda suka bayyana hakan a matsayin nasara ga kamfanin.