Wata budurwa a yanar gizo ta koka kan yadda kasuwancinta yake samun koma baya, inda mutane ba suyi mata ciniki.
Budurwar mai suna Benyiwah Amoah ta sanya wani bidiyo a manhajar TikTok inda ta nuna yadda ta cika shagonta da kaya sannan tace mutum ɗaya kawai yayi mata ciniki. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Wata mata ta mayar da ƴar tsana jika bayan ƴarta ta ƙi haiho mata jika
Ta koka kan cewa rana ta fara takewa a lokacin inda ta tsaya tana tunanin ko menene matsalar kasuwancin nata da mutane ba su zuwa suna mata ciniki.
Daga cikin bidiyon ta, an fahimci cewa tana siyar da kayan amfanin yau da kullu irin su shinkafa, taliya, man girki da dai sauran su.
Bidiyonta ya karaɗe yanar gizo, inda kusan sama da mutum dubu ɗari suka kalle shi.
Wasu daga cikin mutanen da suka kalli bidiyon sun tambayeta a inda shagon yake yayin da wasu suka bata shawarwarin yadda zata magance matsalar dake addabarta.
Mhariyam❤ ta rubuta:
“Abun ban takaicin ma shine mutane na siyar da kaya yanzu da farashin tsofaffin kaya.. Sai Allah ya hukunta ku.. Macuta kawai.”
solomon bonsu ya rubuta:
“Kin ci sa’a ma da har wani yazo yayi siyayya a wajenki. Son zuciya sai ya sanya kasuwancinki ya durƙushe.”
Bra Quabena ta rubuta:
“Ki samu wani natsatstsen ɗaki ko waje ki gayawa ubangiji kukan ki. Faɗin matsalar ki a yanar gizo ba abunda zsi yi miki… Shawara ce na baki.”
eveadams755 ta rubuta:
“Ba ku ga komai ba tukunna, da me zamu riƙa amfani wajen siyan kayyayaki tunda yanzu kun ƙi ku sauke farashin kaya.”
An Gurfanar Da Wani Magidanci Gaban Kotu Saboda Ya Ƙaro Aure
A wani labarin na daban kuma, an maka wani magidanci a gaban kotu saboda ya ƙaro aure.
Ƴan sanda a ranar Laraba sun gurfanar da wani mutum mai suna Edmund Uzoma, a gaban kotun majistare dake Yaba, jihar Legas, bisa zargin ya ƙara aure.
An gurfanar Uzoma a gaban majistare Adeola Olatunbosun bisa tuhomomi guda uku na ƙara auren mace ta biyu da bayar da bayanan ƙarya a jikin katin shaidar aure.