Ƴan sanda a ranar Laraba sun gurfanar da wani mutum mai suna Edmund Uzoma, a gaban kotun majistare dake Yaba, jihar Legas, bisa zargin ya ƙara aure.
An gurfanar Uzoma a gaban majistare Adeola Olatunbosun bisa tuhomomi guda uku na ƙara auren mace ta biyu da bayar da bayanan ƙarya a jikin katin shaidar aure. Jaridar The Punch ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Kotun Allah Ya’isa Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Aniyar Ahmed Lawan Na Tsayawa Takaran Sanata
Mai shigar da ƙara Idowu Osungbure, ya gayawa kotu cewa Uzoma, duk da Uzoma yana da mata, yaje yayi wani auren da wata mai suna Sophia Yongxian, a ofishin rajistar aure.
Ya kuma yi nuni da cewa wanda ake tuhumar yayi ƙaryar cewa baya da mata alhalin akwai aure a kansa.
Osungbure yayi zargin cewa Uzoma ya aikata laifin ne a shekarar 2019, inda ya ƙara da cewa laifin ya cancanci hukunci a ƙarƙashin kundin dokokin jihar Legas.
Tuhumar da ake masa na cewa:
“Cewa kai, Edmund Uzoma, mazaunin Lekki Road 15, Golden Gate Apartment, Lagos, wani lokaci cikin shekarar 2019 a Legas, ka haɗa baki da wasu wajen aikata laifin yin aure kan aure, da bayar da bayanan ƙarya.”
Wanda ake tuhumar ya musanta tuhumomin da ake masa.
Majistare Olatunbosun ta bayar da belinsa kan kuɗi naira miliyan ɗaya, wanda wasu mutum biyu zasu tsaya masa.
Tace dole sai ɗaya daga cikin waɗanda za su tsaya masa yana da gida a Legas.
Olatunbosun ta ɗage sauraron ƙarar har zuwa ranar 15 ga watan Maris, 2023.
Hukumar ICPC Ta Cafke Wata Budurwa Mai Siyar Da Sababbin Takardun Kuɗin Naira
A wani labarin na daban kuma, wata budurwa ta shiga hannun hukumar ICPC bisa zargin siyar da sababbin takardun kuɗin naira.
Hukumar hana cin hanci da rashawa ta Independent Corrupt Practices and Other Related Offences Commission (ICPC), a ranar Talata ta cafke wata budurwa mazauniyar Abuja, mai suna Oluwadarasimi Omoseyin, mai amfani da sunan @SimisolaGold da Simisola of Lala, a Twitter, bisa siyar da sababbin kuɗaɗe a yanar gizo.
Majiyar mu ta samo cewa duk da dai Omoseyin bata bayar da sunayen sauran abokan harƙallar ta ba, tana bayar da haɗin kan da ya dace domin gudanar da bincike.