A yammacin ranar Asabar ne dai wasu ‘yan bindiga suka far wa kauyen Ruwan Tofa, inda suka yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 20.
Mazauna garin sun ce mahara fiye da 200 ne a kan babura suka far wa garin tare da buɗe wuta kan mai uwa-da-wabi lokacin da suka yi yunkurin artabu da su.
Wani mutumin Ruwan Tofa ya shaida wa manema labarai, cewa daga cikin mutanen da aka kashe har da wata mace ɗaya, da kuma maza 20, yayin da mutane 15 suka ji rauni.
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara dai ta ce zuwa yanzu ta tabbatar da mutuwar mutum goma ne sakamakon wannan hari na yammacin Asabar.
Mai magana da yawun ‘yan sandan Zamfara, SP Muhammad Shehu ya ce baya ga mutum 10 da suka tabbatar an kashe, sun samu rahotannin gano ƙarin waɗanda suka mutu wasunsu bayan an su asibiti.