Omoregie Ogbeide Ihama ya janye karar da ya kai kotu tare da marawa Gwamna Godwin Obaseki baya a zaben neman takarar kujerar gwamnan jam’iyyar PDP a jihar Edo.
Omoregie Ogbeide ya janye wa Obaseki ne a ranar da ake zaben dan takarar jam’iyyar PDP gabanin zaben gwamna jihar na watan Satumba.
Ya kuma ce zai janye karar da ya kai na neman kotu ta hana gwamnan shiga zaben fitar da gwanin, bayan a baya ya lashi takobin ba zai janye daga zaben ba.
Kafin janyewarsa, Omoregie Ogbeide ya kai karar ne bisa hujjar cewa dadewar Gwamnan Obaseki a jam’iyyar PDP ba ta kai ta ba shi damar tsayawa takara ba.
Obaseki ya shiga sahun ‘yan takara a zaben a jam’iyyar PDP ne bayan uwar jam’iyyar ta yi masa rangwame jim kadan bayan shigowarsa jam’iyyar.
Gwamnan ya shiga jam’iyyar PDP ne bayan tsohuwar jam’iyyarsa ta APC ta hana masa shiga zaben fitar da gwani gabanin zaben gwamnan da ke tafe wa watan Satumba.
Sai dai wasu masana siyasa na ganin cewa gwamnan zai iya samun nasara a zaɓen fidda gwanin da za a yi duba da irin tasirinsa a siyasar jihar.