Hukumar farin kaya ta Civil Defense ta kama wani mutum mai suna Ahmadu Yaro a ranar Litinin da ta wuce, tare da gurfanar da shi a gaban kotu a jihar Nassarawa.
Shugaban hukumar reshen jihar Nasarawa Dakta Muhammad Gidado Fari ne ya bayyanawa manema labarai a safiyar Larabar nan.
A cewarsa, kotun ta amince su ci gaba da rike mutumin a hannunsu har lokacin da za a yanke hukunci.
“Mutumin ya je gidan su jaririyar ne wata uku da suka gabata inda take kwance tsakanin mahaifanta amma ya dauke ta ya yi mata fyade. Lamarin ya yi muni sosai domin har hanjinta sai da ya fito.
https://dimokuradiyya.com.ng/laifukan-fyade-42-aka-tura-kotu-hukumar-yan-sandan-jihar-kano/
Da farko an kai ta asibitin Dalhatu Arab da ke jihar Nasarawa, amma da batun ya gagare su an tafi da ita asibitin Jami’ar Jos inda ake sa ran yi mata aiki sau tara”, cewar Dakta Muhammad Gidado Fari.
Ya kara da cewa yanzu an sallame su daga asibiti amma za su koma ranar 29 ga watan Yuni.
Batun fyade yana ci gaba da tayar da hankalin jama’a a Najeriya, inda ake samun labaran wannan mummunar dabi’a daga sassa daban-daban na kasar.