Shugaban kwamitin sulhu na jam’iyyar APC a karkashin gwamna Mai Mala Bunin a jihar Yobe, a ranar Alhamis sun ziyarci jigo a jam’iyyar Asiwaju Bola Tinubu a wani mataki na sasanta ‘ya’yan jam’iyyar.
Mamman Mohammed, Kakakin gwamnan Yobe din, shi ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce sun kai ziyarar ne domin ganin sun sasanta ‘ya’yan APC din.
Daga cikin wadanda suke tawagar sun hada da gwamnan jihar Kebbi, kuma shugaban kungiyar gwamnoni ta PGF, Sanata Abubakar Bagudu, sai gwamnan Neja Alh. Abubakar S. Bello da kuma gwamnan jihar Legas Babajide San-Olu.
Kafin nan ma, sai da kwamitin ya ziyarci tsohon shugaban hadakar jam’iyyar, Cif Bisi Akande. Jam’iyyar ta APC ta fada cikin rikici ne tun bayan da aka dakatar da Kwamared Adam Oshiohmole daga shugabancin jam’iyyar, tare da ayyana Victor Giadom a matsayin shugaban jam’iyyar na riko. A inda su kuma kwamitin majalaisar koli na jam’iyyar ta kasa, NWC suka ayyana mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin Kudu, Sanata Abiola Ajimobi a matsayin shugaban jam’iyyar na riko. Sai kuma mataimakin shugaban jam’iyyar na Kudu maso Kudu, Hilliard Eta, aka zabe shi a matsayin shugaban jam’iyyar.
Daga karshe, kwamitin zartaswa ta kasa, NEC ta jam’iyyar, a karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da dukkanin membobin NWC din, inda ya ayyana Gwamna Buni a matsayin shugaban majalisar jam’iyyar na riko.