Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa matasan Nijeriya da ba su wuce shekaru 20 zuwa 40 ba, sune a sahun gaba wajen yada annobar cutar korona, a yayin da mafi yawan wadanda kuma cutar ta fi illartawa su ne ‘yan shekaru sama da hamsin (50).
Babban Daraktan cibiyar dakile cututttuka masu yaduwa, NCDC, Dr Chikwe Ihekweazu shi ne ya tabbatar da hakan a birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis a wani taro na 48 na kullum da kwamitin lura da dakile annobar korona na shugaban kasa ke shiryawa.
Ya sake tunatar da ‘yan Nijeriya cewa har yanzu dokar hana haduwa wuri guda, tana nan, inda ya ce akwai bukatar kowa da kowa su nunawa wadannan tsoffi soyayya ta hanyar kare su daga annobar cutar Korona.