Daraktan yada labarai na hedikwatar tsaron Nijeriya, Manjo Janar John Enenche ya bayyana cewa rundunar sojin ba ta san masu daukar nauyin Boko Haram ba. Ya bayyana hakan ne a yayin da yake ganawa da ‘yan jarida akan ayyukan sojojin a fadin kasarnan.
Manjo Janar John Enenche ya ce; “Da zarar mun samu bayanai daga wadanda muka yi hadin guiwa, muna kai harin soji ne kawai, amma maganar masu daukar nauyinsu (Boko Haram), wannan yana sama ne, bamu gansu ba, sannan bamu ga mutanen da suke daukar nauyinsu ba.” ya tabbatar.
Ya tabbatar da cewa; abin da yake a bayyane shi ne, ‘yan ta’adda suna rike makaman da bai kamata a ce an same su a hannunsu ba. “Ko da kuwa a ce suna sata da kuma siyar da shanu.” Inji shi.
Ya kara da cewa irin muggan makaman da suke rikewa ya isa ya tabbatar da cewa daukar nauyinsu ake yi, inda ya ce amma binciken su wane ne ke daukar dawainiyyarsu, wannan ba aikin soja bane.