Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya tsohon gwamnan jihar Ribas, Chief Rufus Ada-George murnar cika shekara 80 a duniya.
Shugaban kasar a takardar murnar da ya aikawa tsohon gwamnan, ya bayyana shi a matsayin wani mutum abin koyi wanda yake shugaba ne nagartacce.
Shugaban ya bayyana hakan ne ta hannun Kakakinsa Malam Garba Shehu a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Asabar a Abuja, inda ya jaddada cewa Chief Rufus Ada-George mutum ne wanda yake gogaggen dan siyasa wanda ya san shugabanci.
Tsohon gwamnan, yana da sarautar Peripelebo 1 na Okrika, inda shugaba Buhari ya yi masa addu’ar Allah ya kara masa lafiya da tsawon kwana domin ganin kyakkyawan sauyi a kasar da yake matukar so da ma al’ummarsa baki daya.
Buhari ya jinjinawa Ada-George bisa sadaukarwarsa wajen bunkasa zaman lafiya a rikice-rikicen Neja Delta