Gamayyar Hadin Kan Kungiyoyin Kare Hakkin Bil’adama Sun Nemi UN, EU Su Sanya Baki Kan Lamarin El-Zakzaky
Gamayyar kungiyoyin fararen hula da na kare hakkin bil’adama sun rubuta wasika zuwa ga majalisar dinkin duniya (UN) da kuma hukumar kare hakkin bil’adama ta kungiyar Tarayyar Turai (EU) suna mai neman su yi kira ga gwmanatin Nijeriya ta kawo karshen danniya da suka yiwa ‘yan shi’a da shugabansu Shaikh Ibraheem Zakzaky.
Hakan na dauke ne a cikin sanarwar da membobin wadannan kungiyoyi suka sanyawa hannu, wanda ya hada da Geoffrey N Nwokolo (Esq), Prince Adelaja Adeoye, Dr Hassan Bala, Kwamared E. Ekoja, Kwamared C. Mabel, da kuma Kwamared Ahmad Shuaib, inda suka bayyana cewa hukumomin Nijeriya sun gaza yin adalci kan kisan kiyashin da aka yiwa ‘yan shi’a a Nijeriya tun daga ranar 12 ga watan Disambar 2015. Inda suka ce; “a lokacin da sojojin Nijeriya suka yi amfani da karfin gaske wajen dirarwa ‘yan shi’ar a Zariya dake jihar Kaduna a arewa maso yammacin Nijeriya.” Inji su.
Sanarwar ta ci gaba da cewa; “A lokacin wannan harin, sojoji sun kashe daruruwan membobin wannan kungiya, inda kuma suka kama daruruwansu ciki kuwa harda jagoransu, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, da matarsa Zeenat Ibraheem.” Suka tabbatar.
Kungiyar ta bayyana cewa hakan take ‘yancin bil’adama ne na ‘yan shi’ar Nijeriyar a karkashin jagorancin Sheikh Ibraheem El-Zakzaky. A cewarsu ‘yancin dukkanin wani mutum ciki kuwa harda wanda ake zargi, da wadanda ake tsarewa da kuma daurarru a gidajen yari abin a girmama ne a kowanne lokaci; “kuma dukkan wadanda ake bincike ake kuma ci gaba da tsare su, dole ne a kare lafiyar jikinsu tare da dukkanin wata barazana da take fuskantarsu, kuma a guji sanya musu karfi da dukkanin wani halayya da zai take ‘yancinsu, tare da bin dukkanin ka’idojin da aka gindaya a cikin kundin tsarin mulkin Nijeriya da sauran dokokin duniya wanda Nijeriya ta sanyawa hannu na haramta horo.” Inji sanarwar kungiyar.
Kungiyar ta ce kisan kiyashi, rushe-rushen muhalli da kuma kamu ba bisa ka’ida ba, ya sabawa dokokin Nijeriya na kare ‘yancin bil’adama na ‘yan kasa dake cikin shafi na IV na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999.
A karshe kungiyar ta yi tir da abin da ta kira take ‘yancin ‘yan shi’ar da shugabansu, Shaikh Zakzaky da matarsa Zeenat, wadanda suka ce ana ci gaba da tsare su da harsasai a jikinsu.